Ana zargin Chelsea da badakala

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Christian Atsu na daga 'yan wasan Chelsea da ke zaman aro a Vitesse Arnhem

Hukumar kwallon kafa ta Holland tana binciken alakar Chelsea da kungiyar Vitesse Arnhem ta kasar kan zargin wata kumbiya-kumbiya.

Binciken ya biyo zargin da tsohon me kungiyar ta Vitesse Arnhem ya yi ne a wata jarida cewa Chelsea ba ta so kungiyar ta samu shiga gasar Zakarun Turai ba.

A shekarunnan Chelsea ta kulla dangantakar wasa da kungiyar ta Netherlands da har take tura mata 'yan wasa aro.

A ka'idar Uefa kungiyoyi biyu da ke da mamallaki daya ba za su shiga gasa daya ba.

Hukumar kwallon Holland ta tuntubi Vitesse domin karin bayani za ta kuma duba batun mallakar kungiyar.

Tsohon babban me hannun jari a kungiyar Merab Jordania ya gaya wa jaridar kasar De Telegraaf cewa Chelsea ta bukaci klub din da ka da ya ci kofin Eredivisie.

Don ka da ya samu damar shiga gasar Zakarun Turai.

Haka kuma mutumin da ya mallaki kungiyar ta Vitesse a yanzu Alexander Chigrinsky yana da alaka da me Chelsea Roman Abramovich.

Ya zuwa yanzu dai Chelsea ba ta ce komai ba gme da zargin.