Pique zai yi jiyyar sati hudu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Minti 12 da fara wasan ne Gerard Pique ya fice daga fili saboda raunin

Dan wasan Barcelona Gerard Pique zai yi jiyyar makwanni hudu sakamakon raunin da ya ji a kugunsa a wasansu da Atletico Madrid na Kofin Zakarun Turai.

Pique me shekaru 27 ya yi mummunar faduwa ne bayan da suka tashi sama da Diego Costa, wanda shi ma daga baya aka fitar da shi a wasan da suka tashi 1-1.

Yanzu dan wasan ba zai buga karo na biyu na wasan da Atletico Madrid ba na matakin dab da na kusa da karshe na Zakarun Turan ba, da kuma na Copa Del Rey da Real Madrid ranar 16 ga watan Afrilu.

A halin da ake ciki kuma kociyan Atletico Diego Simeone na cike da damuwa saboda halin rashin tabbas na dan wasan da ya fi ci masa kwallo Diego Costa.

Costa ya ci kwallaye 33 a bana kuma rashinsa a haduwa ta biyu da Barcelona ranar tara ga watan Afrilu a gidan Atletico babbar matsala ce.