Real Madrid ta doke Dortmund

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Borussi Dortmund na da jan aiki a gabanta a karawa ta biyu ran Talata saboda rashin sa ko da kwallo daya a raga

Real Madrid ta kama hanyar zuwa wasan kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai karo na hudu bayan da ta yi nasara kan Borussia Dortmund da ci 3-0.

Kungiyar ta fara wasan da sa'a inda minti uku da shiga fili Gareth Bale ya daga ragar Dortmund.

Bayan wasu mintuna 22 ne kuma sai Isco ya kara ta biyu da wata kwallo da ya sheko ta kasa.

Dawowa daga hutun rabin lokaci a minti na 57 sai Ronaldo wanda wannan ne wasansa na 100 a gasar Zakarun Turan, shi ma ya samu damar jefa tashi.

Kwallon dai ita ce ta 14 da ya ci a gasar ta Zakarun Turai a bana,wanda da hakan ya kamo Lionel Messi.