Tottenham za ta gina babban filin wasa

Hakkin mallakar hoto Tottenham
Image caption Sabon filin wasan Spurs

Tottenham Hotspur na saran kammala sabon katafaren filin wasanta a shekara ta 2017 mai cin 'yan kallo 58,000.

Sabon filin wasan zai kasance kusada filinta na yanzu wato White Hart Lane mai cin 'yan kallo 36,000.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta Tottenham ta sanarda samun ribar fan miliyan daya da rabi shekarar da ta wuce.

Kungiyar na ganin cewar idan har ta gina babban filin wasa, za ta samu karin kudaden haraji don ci gaba da goggaya da sauran manyan kungiyoyin Turai.

Shugaban Spurs, Daniel Levy ya ce babban mataki ne ga kungiyar idan aka kamalla babban filin wasan.