Benteke ba zai je wasan duniya ba

Image caption Benteke ya buga wa Belgium wasa na karshe da suka ci Scotland a watan Satumba na 2013.

Dan wasan Aston Villa na gaba kuma dan Belgium Christian Benteke ba zai yi wasa tsawon watanni shida ba saboda rauni.

Za a yi wa dan wasan me shekaru 23 tiyata a ciwan da yaji a kafarsa lokacin atisaye.

Sakamon wannan raunin da ya ji ba zai je wasan kofin duniya a Brazil ba.

Benteke ya koma Aston Villa a watan Agusta na 2012 a kan kudi fam miliyan 7 daga kungiyar Genk ta Belgium.

Dan wasan ya ci kwallaye 23 a dukkanin gasar da ya buga wa Villa a kakar farko a Ingila kuma ana cewa zai bar kungiyar.

A bana ya ci kwallaye 11, kuma da ana saran za a sa shi cikin tawagar 'yan wasan Belgium da za su je gasar kofin duniya.

Ya buga wa Belgium wasa na karshe da suka ci Scotland a watan Satumba na 2013.