Europa: Juventus ta kunyata Lyon 1-0

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bonucci ne ya ci Olypique Lyonn a minti na 85 da wasan

Juventus ta bi Lyon har gida ta lika mata daya me ban haushi a wasan dab da na kusa da karshe na gasar Europa.

Haka ita ma kungiyar Benfica ta bi AZ Alkamaar har gida ta yi mata 1-0.

FC Basel kuwa ta ci bakinta Valencia 3-0, yayin da Porto a gidanta ta yi wa Sevilla 1-0.

A ranar Alhamis me zuwa 10 ga watan Afrilu za a yi karo na biyu na wasannin.