'Rooney ba ya cikin gwanayen duniya'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Barton ya ce, ''idan ka ga Rooney yana shan taba za ka ce yana yin abin ya kamata ya zama gwarzon dan wasa na duniya?''

Wayne Rooney ba shi da natsuwar da zai iya zama gwanin dan wasan duniya inji Joey Barton.

Barton, dan wasan tsakiya na QPR, wanda yana sha'awar wasan Rooney, ya ce, dabi'arsa a fili ce matsalarsa.

Dan wasan me shekaru 31, ''ya ce duba halayyarsa.

Ka kwatanta shi da Cristiano Ronaldo za ka ga bambanci matuka.''

Sai dai kuma tsohon dan wasan na Man City da Newcastle ya ce, gazawar ta Rooney na daga matsalar kwallon kafar Ingila.