Odemwingie ya sasanta da Keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Osaze Odemwingie

Dan kwallon Nigeria, Peter Odemwingie ya ce ya dunke barakar dake tsakaninsa da kocin Super Eagles Stephen Keshi.

Sun samu sabani ne lamarin da ya sa aka ki kiran Odemwingie don bugawa Nigeria gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu, abinda ya kaiga dan kwallon ya yi wasu kalamai a shafinsa na Twitter.

Odemwingie yace "A yanzu muna magana da kocin kuma komai ya wuce".

A lokacin dai Odemwingie ya zargi Keshi da raina masa wayo, shi yasa aka shafe watanni 16 ba a gayyaceshi a tawagar Super Eagles ba.

A 'yan makwannin nan Odemwingie yana haskakawa a tawagarsa ta Stoke a cikin gasar Premier ta Ingila.

Karin bayani