Schumacher na nuna alamun farfadowa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a bara Schumacher yake a sume

Rahotanni sun ce tsohon zakaran tseren motocin nan na Formula One, Michael Schumacher, wanda ya yi wata doguwar suma, sakamakon zamewar da ya yi a kan kankara, yanzu ya fara nuna alamun farfadowa a asibiti.

Wakiliyarsa, Sabine Kehm ta ce Schumacher yana samun sauki, amma ta ce ba za a bada wani karin bayanai a kan halin da yake ciki ba.

Likitoci na kokari ne su ga ko Schumacher din zai dan matse hannunsa ko kuma zuciyarsa za ta buga fiye da a yanzu.

Wakilin BBC ya ce Likitoci na kokarin fitar da shi daga doguwar suma da ya yi, kuma wannan sakamako zai ba danginsa kyakyawan fata ya samu sauki.

A cikin watan Disamba ne dai, Schumacher, wanda ya lashe gasar ta Formula har sau 7, ya ji rauni ne a ka, a lokacin da yake zamiyar kankara a tsaunikan Alpes na Faransa.

Karin bayani