An ci tarar kungiyar Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallon Koriya ta Kudu, Ji Dong-Won

Hukumomin gasar Premier ta Ingila sun ci tarar Sunderland saboda saka wani dan kwallon da bai dace ba a gasar.

Dan wasan Ji Dong-Won ya buga wasanni hudu tare da Sunderland a gasar Premier kafin mahukunta kulob din su bayyana cewar ya dawo yana buga musu kwallo daga aron da suka bada shi.

Kamata yayi Sunderland ta bayyana cewar Dong-Won wanda ya tafi aro a kungiyar Augsburg ya koma taka mata leda amma bata nemi izinin hukumar gasar Premier ba.

Kawo yanzu gasar hukumar gasar Premier ta Ingila bata ce komai ba akan batun.

Sunderland ta sayi Ji Dong-Won ne daga kungiyar Chunnam Dragons ta Koriya ta Kudu a shekara ta 2011.