Anelka ya koma Atletico ta Brazil

Image caption Ana danganta alamar da ya yi da hannunsa da kin jinin yahudawa

Tsohon dan wasan Faransa Nicolas Anelka ya koma kungiyar Atletico Mineiro ta Brazil.

Anelka mai shekaru 35 ya kasance ba shi da kungiya tun lokacin da West Brom ta kore shi wata daya da ya wuce.

Bayan da yayi wata alama ta nuna kin jinin yahudawa lokacin da yake murnar cin kwallo, a wasan da suka yi 3-3 da West Ham

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ita ma ta hana dan wasan buga wasanni biyar tare da cin tararsa fan dubu 80 kan laifin.

Shugaban kungiyar ta Brazil Alexandre Kalil shi ya sanar da komawar dan wasan ta shafin Intanet na Tweeter.

Ko da ike dai kungiyar ta Atletico Mineiro ba ta fito da kanta ta sanar ba.