Everton ta buge Arsenal 3-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rabon da Everton wadda ta kasance a gida ta ci Arsenal tun 2007.

Everton na dab da cika alkawarin kociyanta Roberto Martinez na samun gurbin gasar Zakarun Turai bayan ta doke Arsenal 3-0.

Steven Naismith ne ya jefa kwallon farko a minti na 14 bayan tare wata kwallo da Romelu Lukaku ya sheko.

A minti na 34 ne kuma sai Lukakun ya yi nasarar daga ragar Arsenal din da kwallo ta biyu, wadda iat ce ta 14 a kakar nan.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Mikel Arteta na Everton a da dan Spaniya ya ci kansu da kwallo ta uku.

Arsenal ce ta hudu yanzu da maki 64 a wasanni 33, yayin da Everton ke mara mata baya da maki 63 amma da wasanni 32.

Duk da cewa Everton a gaba za ta hadu da Man City da kuma Man United a gida, ganin yadda ta yi da Arsenal, magoya bayanta na ganin alkawarin zuwa gasar Zakarun Turan zai cika.

Karin bayani