Norwich ta kori kociyanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar ta ce ta sallami Hughton ne domin ta tsira a gasar Premier bana.

kungiyar Norwich ta sallami kociyanta Chris Hughton ta maye gurbinsa da mai horad da matasan 'yan wasanta Neil Adams.

Kungiyar ta yi rashin sa'a a karawarsu da West Brom ranar Asabar da ci 1-0.

Kuma maki biyar ne tsakaninta da matakin faduwa daga Premier yayin da ya rage wasanni biyar a kammala gasar.

Kungiyar za ta yi wasa da Fulham da Liverpool da Manchester United da Chelsea da kuma Arsenal a na gaba.

A bara Hughton mai shekaru 55 ya jagoranci kungiyar ta kare a matsayi na 11 a Premier.

Kuma ta ce ta sallame shi ne domin ta tsira a gasar a bana.