Liverpool ta sake hawa teburin Premier

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Liverpool na matsayi na daya yayin da West Ham ke na 11

Kungiyar Liverpool ta sake hawa teburin Premier bayan ta bi West Ham United har gida ta ci ta 2-1.

Steven Gerrard ne ya fara daga raga a bugun daga-kai-sai-maitsaron-gida a minti na 44 bayan James Tomkins na West Ham ya taba kwallon da hannu.

Sai dai nasarar ba ta yi nisa ba domin minti daya tsakani ne sai Guy Demel ya rama, yayin da 'yan Liverpool ke korafin cewa Andy Carroll ya yi laifi a kan mai tsaron gidansu Simon Mignolet.

Carroll ya kai wani hari da kwallon ta bugi sandar raga a kashi na biyu na wasan.

Amma can a minti na 71 Liverpool ta sake samun fanareti bayan maitsaron gidan United ya kayar da Jon Flanagan.

Daga nan ne kyaftin din Liverpool Gerrard ya sake bugawa ya kuma jefa ta a raga.

Yanzu Liverpool ta sake zama ta daya da maki 74 a wasanni 33, a gaban Chelsea mai maki 72.

West Ham United tana matsayi na 11 da maki 37 a wasanni 33.