Zamu ba Bayern mamaki- Evra

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Evra ya ce, ''wajibi ne mu tabbatar magoya bayanmu sun yi alfahari da wasanmu na biyu a Bayern.''

Patrice Evra ya ce abin takaici ne Manchester United kofi daya kawai take fafutukar nema yanzu, amma yana fatan za ta yi koyi da nasarar Chelsea ta Zakarun Turai a 2012.

United wadda a gida ta yi kunnen doki 1-1 da Bayern Munich me rike da kofin Zakarun Turan , za su fafata a karo na biyu na wasan dab da na kusa da karshe ranar Laraba.

Shekaru biyu da suka uce Chelsea ita ce ta shida a tebur matsayin da Man United take a yanzu, amma ta dauki Kofin Zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 32 bai buga wasan farko ba da kuma wanda United ta ci Newcastle 4-0 ranar Asabar saboda ciwon guiwa amma ana saran zai yi wasan na Munich.

Man United ta fi kowa samun kyakkyawan sakamako a waje a gasar Premier ta bana, amaa kuma ta na fama a gida.