Oscar Pistorious ya yi nadama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pistorious ya ce ya harbi budurwar tasa ce kan kuskuren barawo ne ya shigo masa gida

Cikin hawaye, zakaran tseren nan dan Afirka ta kudu, Oscar Pistorious ya nemi gafara yayin da ya soma ba da bahasi a shari'ar tuhumar aikata kisan da ake yi ma sa.

Ya kuma fadawa kotun cewa, tun daga lokacin da ya harbe buduwarsa Reeva Steenkamp, ko yaushe yana tunanin iyalanta.

Muryarsa tana rawa, Oscar Pistorious ya kuma fada wa kotun cewa, yana jin abin da takaicin abin da ya haddasa:

A Wasu lokutan da kyar zakaran tseren kan furta kalmomi, a farkon ba da bahasin da zai dau kwanaki.