Ban da tabbas na zuwa Brazil - Taiwo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taye Taiwo

Dan kwallon Bursaspor Taiye Taiwo ya ce da kamar wuya, Nigeria ta gayyaceshi ya buga mata gasar cin kofin duniya a Brazil.

Dan wasan wanda ya buga wa kungiyarsa wasanni 34 a Turkiya a kakar wasa ta bana, a halin yanzu kuma yana fuskantar kalubale daga wajen Elderson Echiejile don taka leda tare da Super Eagles.

Taiwo yace "Na buga gasar cin kofin duniya a 2010, amma a yanzu da kamar yuwa in buga".

Duk da cewar Echiejile baya samun damar bugawa kungiyarsa ta Monaco a kakar wasa ta bana, amma dai bisa dukkan alamu shi ne wanda aka fi saran zai je gasar cin kofin duniya.

A mako mai zuwa ne ake saran kocin Super Eagles, zai sanarda da tawagar 'yan kwallon da za ta je gasar cin kofin duniya a Brazil.

Taiwo mai shekaru 28, ya shafe kusan shekaru biyu ba tare da an gayyaceshi cikin tawagar Super Eagles ba.

Taiwo wanda ya soma bugawa Nigeria a shekara ta 2004, ya buga gasar cin kofin Afrika a 2006, 2008 da kuma 2010.

Ya taka leda a kungiyoyi a Faransa da Italiya da Ingila da Ukraine da kuma Turkiya.