Tottenham ta doke Sunderland 5-1

Hakkin mallakar hoto
Image caption Burin kociyan Tottenham Tim Sherwood ya kai kungiyar gasar Zakarun Turai

Tottenham ta kara jefa Sunderland tsaka-mai-wuya bayan da ta doke ta 5-1.

Sunderland ta karshe a tebur ta fara wasan da kyau bayan da Lee Cattermole ya ci mata kwallonta minti 17 da shiga fili.

To amma minti 11 tsakani sai Adebayor ya rama daga wata kwallo da Eriksen ya kwararo ta gefe.

Bayan hutun rabin lokaci a minti na 59 sai Kane ya kara ta biyu, kafin Eriksen shi ma ya ci tasa ta uku.

Minti hudu kafin cikar lokaci sai Adebayor ya kara ta hudu.

Sannan kuma bayan cikar lokacin mintuna casa'in sai Sigurdsson ya jefa kwallon ta biyar.

Da wannan nasara Tottenham ta zama ta shida a tebur gaban Man United ta bakwai da maki 59 a wasanni 33.

Sunderland kuwa ta cigaba da kasancewa ta karshe da maki 25 a wasanni 31.