Karon Tottenham da Sunderland

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adebayor ya ce yana fatan taimaka wa Tottenham ta kammala kakar bana da kyakkyawan matsayi a Premier

A wasan da Tottenhm za ta yi da Sunderland ranar Litinin din nan wasu daga cikin zaratan 'yan wasanta da suka tafi jiyya za su dawo fage ciki har da Adebayor.

Vlad Chiriches and Paulinho na daga wadanda za su yi wasan amma kuma Roberto Soldado and Jan Vertonghen ba za su buga ba saboda raunukan da suka ji a karshen makon da ya gabata.

To amma shi kuwa kociyan Sunderland Gus Poyet ba shi da wata damuwa ta raunin 'yan wasa yayin da zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa.

Sunderland dai tana cikin tsaka-mai-wuya a matsayin ta karshe a tebur da tsiran maki bakwai tsakaninta da ficewa daga hadarin faduwa daga Premier.

Sunderland na fafutukar samun maki saboda maki daya kawai ta samu a wasanninta shida da suka gabata.

Kuma a ziyararta zuwa gidan Tottenham a manyan wasanni 19 sau daya kawai ta taba samun nasara da 2-1 a watan Agusta na 2008.

Kungiyar ce ta ashirin da maki ashirin da biyar a wasanni talatin.

Sai dai yanayin kwazon Tottenham din a yanzu ka iya bai wa tsohon dan wasan nata Poyet kwarin guiwa.

A wasanninta hudu na Premier a baya bayannan Tottenham ta yi rashin nasara a guda uku.