UEFA: Zamu fitar da PSG - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho

Kocin Chelsea , Jose Mourinho ya ce kungiyarsa za ta iya lallasa Paris St Germain don kaiwa zagayen kusada karshe a gasar zakarun Turai.

A bugun farko da suka buga a birnin Paris, PSG ta doke Chelsea daci uku da daya, amma kocin Blues na ganin cewar za su iya tsallakewa.

Mourinho yace "Ina da kwarin gwiwa a kan 'yan wasana kuma karawar na da mahimmanci gare mu".

Ana saran Samuel Eto'o zai koma taka leda bayan jinyar da ya yi.

Shi kuwa kocin PSG, Laurent Blanc cewa yayi kungiyarsa za ta baiwa Chelsea mamaki a birnin London.

Karin bayani