Jamhuriyar Ireland za ta kara da Ingila

Hakkin mallakar hoto INPHO
Image caption Ingila ta yi nasara a biyar kuma ta sha kashi a biyu daga cikin wasanni 14 da ta yi da Jamhuriyar Ireland.

Jamhuriyar Ireland za ta karbi bakuncin Ingila a wasan sada zumunta na kwallon kafa a Dublin a watan Yuni na 2015.

Kungiyoyin biyu sun hadu a Wembley a watan Mayu na na 2013 kuma hukumar kwallon kafa ta Ireland ta ce an yi yarjejeniyar sake wasan a Dublin.

Rabon da Ingila ta yi wasa a Ireland tun 1995, lokacin da aka dakatar da wasan sada zumunta tsakaninsu saboda rikicin 'yan kallo.

Wannan haduwar da za su yi a watan na Yuni shi ne karon farko da Ingila za ta je filin wasa na Aviva inda za a yi wasan.

Wasan sada zumuntar da suka yi a shekarar da ta wuce sun tashi 1-1, inda Frank Lampard ya rama wa Ingila bayan Shane Long ya ci wa Ireland.