Rodriguez ba zai je Brazil ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jay Rodriguez

Dan kwallon Southampton Jay Rodriguez ba zai buga gasar cin kofin duniya ba saboda rauni a gwiwarsa.

Dan wasan mai shekaru 24 ya ji rauni ne a wasansu da Manchester City a ranar Asabar da ta wuce.

A yanzu haka dai ana saran zai koma taka leda a watan Okotoba idan ya murmure daga raunin.

Kafin rauninsa an zaci Ingila za ta saka shi cikin tawagarta zuwa Brazil.

Darektan Southampton Les Reed ya ce "muna fatan ya warke a kan lokaci, amma dai rauni cikas ne gare shi".

Rodriguez mai shekaru 24, ya bugawa Ingila kwallo a karon farko a wasanta da Chile a watan da ya wuce.

Karin bayani