Sherone Simpson ta yi amfani da kwaya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sherone Simpson ta dora alhakin laifin akan kociyanta

An dakatar da 'yar tseren Jamaica ta gasar Olympics watanni 18 saboda amfani da kwayar kara kuzari.

A watan Janairu Simpson mai shekaru 29 ta ce wani magani da mai horad da ita dan Canada ya ba ta shi ne sanadi.

Sai dai 'yan kwamitin yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni na Brazil sun ce sakacin Simpson din ne ya jawo mata.

Ita ma 'yar wasan jifan faifai ta Jamaican Allison Randall an dakatar da ita shekara biyu saboda laifin amfani da kwayoyin kara kuzari.