Bayern Munich ta yi waje da Man U 4-2

Hakkin mallakar hoto g
Image caption Wasan farko ya bai wa Manchester United kwarin guiwa

Zakarun Jamus kuma na Turai Bayern Munich sun fitar da Manchester United daga gasar Zakarun Turai da ci 4-2, jumulla, bayan a karon farko sun yi 1-1 a Old Trafford.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Evra ya fara jefa kwallo a ragar Bayern Munich a minti 57, amma minti biyu tsakanin kacal Mandzukic ya rama wa masu rike da kofin.

Daga nan ne kuma sai 'yan bayan din suka karya lagon bakin nasu inda a minti na 68 Muller ya kara daga ragar Unite da kwallo ta biyu.

Minti takwas tsakani kuma sai Robben ya shigo da'irar Manchester United da kwallo shi kadai ya kacaccala 'yan bayan United ya sheka musu kwallo ta uku.