Man U ta je wurin tuna 'yan wasanta

Hakkin mallakar hoto MANCHESTER UNITED
Image caption 'Yan wasan Manchester United takwas ne suka mutu a hadarin bayan sun dawo daga wasa

'Yan wasan Manchester United sun ziyarci wurin da 'yan wasan kungiyar suka yi hadarin jirgin sama a Munich a 1958 domin martaba su.

Sir Bobby Charlton wanda ya tsira a hadarin shi ne ya jagoranci tawagar 'yan wasan, da su ka je birnin domin wasansu na gasar Zakarun Turai da Bayern Munich.

Dan wasan tsakiya na United Micheal Carrick ya ce ziyarar ta sanyaya jikin 'yan wasan da sa su juyayi.

Carrick ya ce, '' ziyarar aba ce da ta kada mu, ganin tarin magoya bayan United suna rera waka cewa Man United ba za ta taba mutuwa ba.''

Hadarin jirgin saman da ya auku ranar 6 ga watan Fabrairu na 1958 ya hallaka mutane 23 da suka hada da 'yan wasan United takwas.

Hadarin ya faru ne a lokacin da suke dawowa daga wasan Kofin Turai da kungiyar Red Star ta Belgrade.