Shakku kan golan Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Courtois ya yi yarjejeniyar shekaru biyar da Chelsea a 2011 lokacin da ta sayo shi daga Genk amma bai taba yi mata wasa ba.

Mai yuwuwa mai tsaron gidan Atletico Madrid Thibaut Courtois ba zai yi wasa ba idan aka hada kungiyar da Chelsea wadda ta ba da shi aro.

Mai tsaron gidan dan shekara 21, wanda kuma ke yi wa Belgium wasa yana kaka ta uku ke nan a matsayin aro a Atletico wadda ta kai wasan kusa da karshe bayan ta fitar da Barcelona da 2-1.

Idan har zai yi wasan in aka hada Atletico da Chelsea a wasan na kusa da karshe na Zakarun Turai, sai kungiyar ta biya makudan kudade.

Sai dai kuma shugaban kungiyar ta Atletico Enrique Cerezo, ya ce, ''kudi ne da ba za mu iya biya ba.''

A kasar Spaniya an ruwaito cewa kudin da Atletico za ta biya idan zai yi wasan da Chelsea ka iya kaiwa fam miliyan 4.95