Hodgson ya jinjina wa manajoji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hodgson da Townsend

Kocin Ingila, Roy Hodson ya jinjina wa masu horad da 'yan kwallon Everton da na Southampton saboda bai wa matasa dama a gasar Premier.

A cewarsa matakin Roberto Martinez da Mauricio Pochettino ya taimaka wa tawagar 'yan kwallon Ingila.

Hodgson ya ce "Kocin Everton Martinez ya taimaka wajen ajiye Leon Osman ya saka matashi Ross Barkley".

Sannan kuma Pochettino ya nuna jarumta wajen bai wa Luke Shaw dama.

Bayanai kan Ingila:

13 ga watan Mayu: Sanarda sunayen 'yan wasa 23, da bakwai masu jiran tsammani.

30 ga watan Mayu: Ingila v Peru (Sada zumunci)

2 ga Yuni: Tawagar 'yan 23 da za su je Brazil

4 ga Yuni: Ingila v Honduras (Sada zumunci)

7 ga Yuni: Ingila v Ecuador (Sada zumunci)

14 ga Yuni: Wasan farko a Brazil tare da Italiya

Karin bayani