An hana Powell tsere har watanni 18

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Powell ya ce zai daukaka kara a kotun wasanni ta duniya

An haramta wa tsohon zakaran tseren mita 100 na duniya Asafa Powell, shiga gasa har tsawon watanni 18 saboda amfani da kwayar kara kuzari.

Dan tseren na Jamaica mai shekaru 31 ya yi amfani da kwayar ce wadda aka haramta a lokacin gasar tsere ta Jamaican ta bara.

Amma kuma aka ja hukuncin baya da a yanzu zai kare ranar 20 ga watan Disamba na 2014.

Powell ya ce hukuncin rashin adalci ne, domin shi wata kwaya wadda ba haramtacciya ba ce ya sha, wadda aka gurbata a rashin saninsa.

A ranar Talata aka haramta wa Sherone Simpson mai lambar zinariya da ta azurfa a gasar Olympics shiga gasa ita ma kan irin wanna laifi.

Dukkaninsu dai yanzu ba za su halarci gasar wasannin Commonwealth ba da za a yi a Glasgow a watan Yuli.