Gerrard da Suarez sun samu kyauta

Hakkin mallakar hoto Barclays Premier League
Image caption Livrepool na haskakawa a gasar Premier

An baiwa 'yan kwallon Liverpool Steven Gerrard da Luis Suarez kyautar bajinta ta gasar Premier ta Ingila a watan Maris.

Wannan ne karo na shida da aka baiwa mutane biyu kyautar a hade.

Shima kocin tawagar, Brendan Rodgers ya samu kyautar a bangaren masu horadda 'yan wasa a karo na biyu a kakar wasa ta bana.

Liverpool wacce ke kokarin lashe gasar Premier ta zura kwallaye 18 a watan Maris, inda ta doke Manchester United da Cardiff da Southampton da Tottenham da kuma Sunderland.

Wannan ne karo na shida da Gerrard ya samu kyautar sannan kuma Suarez ne ya samu kyautar a watan Disamba.

Karin bayani