Lopez ya ce ba zai bar Real Madrib ba

'Yan wasan real madrid
Image caption 'Yan wasan real madrid

Diego Lopez ya ce, ba zai bar Real Madrib ba sai idan Club din ne ya kore shi da kan sa. ya yi watsi da rahotannin da ake bayar wa cewa, ba ya jin dadi a zaman sa a Real Madrid.

Diego ya maida martani cikin raha yana cewa "ba zan bar kulob din ba, sai an kore ni".

Wasu masharhan ta sun yi ikirarin cewa, mai tsaron gidan dan shekaru 32 da haihuwa yana da takaicin cewa shine mutum na farko da Carlo Ancelotti ya zaba a gasar wasanni ta Liga.

Sai dai kuma Lopez din ya ce, ya fi farin ciki, ya tashi haikan don ya ciwo jersey mai lamba ta 1.

Mujallar wasanni ta Sportyou ta ruwaito yana cewa,"ina da sauran shekaru ukku a kwantaragi na, ba zan bar kulob din ba, sai idan su ne suka kore ni."

Karin bayani