Gerrard: Ina cikin matsin-lamba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Gerrad ya ce, ''ina ji na kamar dan shekara 21, yadda nake wasa da wadannan manyan 'yan wasa.''

Kyaftin din Liverpool Stephen Gerrad ya ce wata mai zuwa ka iya kasancewa lokaci mafi tsanani a rayuwarsa ta kwallon kafa yayin da kungiyarsu ke shirin wasanni hudu a kokarin daukar Premier.

Gerrard ya ce, '' sakon shi ne mu natsu akwai wasanin karshe na kofuna hudu a gabanmu zan yi duk abin da zan iya domin ganin mun sami nasara.''

Kyaftin din na kwatanta kowane wasa daga cikin hudun da suka rage musu a matsayin wasan karshe, domin idan suka rasa daya labarin zai sha bamban.

A ranar Lahadi ne Liverpool ta ci Manchester City 3-2 kuma za ta dauki kofin a karon farko a shekaru 24 idan ta yi nasara a sauran wasanninta hudu.

Nasarar ita ce ta goma a jere da Liverpool ke samu, a ranar da ake cika shekaru 25 da turmutsutsun da aka yi a filin kungiyar ta Liverpool, Hillsborough, da ya hallaka 'yan kallo.

Karin bayani