Micheal Phelps zai dawo daga ritaya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Micheal Phepls zai sake jarraba sa'arsa a gasar Olympics

Tsohon zakaran wasan linkaya na Amurka Micheal Phelps ya ba da tabbacin shirinsa na dawowa fagen wasan daga ritayar da ya yi.

Phelps zai dawo ne domin fara shirin tunkarar gasarsa ta Olympics ta biyar a 2016.

Mai shekara 26 Phelps ya yi ritaya bayan gasar Olympics ta London a 2012, inda ya samu nasarar cin lambobi shida.

Da wannan bajinta ya zama dan wasan Olympics da ya fi samun lambobi a tarihin gasar.