An kawar da bajintar Roger Milla

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roger Milla ya taimaka wa Kamaru ta kai wasan dab da na kusa da karshe na duniya a 1990 bayan ya dawo daga ritaya

Roger Miller ya rasa kambinsa na kasancewa dan wasan kwallon kafa mafi yawan shekaru da ya yi wa wata kasar Afrika wasa, inda yanzu Kersley Appou na Mauritius mai shekaru 43 ya kafa wannan tarihi.

Kafin yanzu Milla ya kafa wannan tarihi ne lokacin da ya buga wa kasarsa Kamaru wasa a karawarta da Russia inda ta sha kashi 6-1 a gasar Kofin Duniya ta 1994 yana da shekara 42 da kwanaki 39.

To amma dai har yanzu Roger Millan zai ci gaba da kasancewa a matsayin tsohon dan wasan da ya fi kowana dan wasa a gasar kofin duniya, kuma wanda ya ci kwallo a gasar.

Shi dai dan wasan na mauritius da ke barazana ga bajintar ta Roger Milla, wato Kersley Appou ya yi wa Mauritius wasa ne a karawarta da Mauritania ta neman shiga gasar kofin kasaashen Afrika ranar Asabar, inda suka yi rashin nasara.

Shi dai Appou shekarunsa 43 da kwanaki 354, wanda har yanzu bai kai Macdonald Taylor Sr na Virgin Islands da ke Amurka ba, wanda shi ne ya kafa tarihin dan wasan da ya fi yawan shekaru a duniya yana da shekara 46 da kwanaki 217.

Roger Milla na Kamaru ya yi wasa a gasar kofin Duniya har uku kuma yana daya daga cikin fitattun 'yan wasan gasar ta 1990 lokacin yana shekara 38 bayan da ya sake dawowa fage daga ritaya ya kuma jagoranci kamaru ta kai wasan dab da na kusa da karshe.