Mun so Liverpool ta doke Man City- John Terry

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea na matsayin ta biyu a bayan Liverpool da maki biyu

Kyaftin din Chelsea John Terry ya ce nasarar da Liverpoll ta yi a kan Manchester City ta yi musu dai-dai a fafutukar da suke yi ta daukar kofin Premier.

Terry, ya ce, '' mun san da sakamakon wasan na Liverpool kuma shi ne kila abin da muke so.''

Dan wasan na baya , ya kara da cewa, ''mun yi nasara a wasanmu, matsin lamba har yanzu na kan kungiyoyin da suke sama da kuma wadanda ke kasanmu.

Mun san cewa za mu saukaka musu lamari idan ba mu ci wasanninmu ba ko da ya sakamakon wasan Liverpool din ya kasance.''

Chelsea wadda za ta ziyarci Liverpool ranar 27 ga watan Afrilu, tana da maki biyar a gaban Man City ta uku, ko da ike City na da bashin wasanni biyu.