Arsenal ta koma ta hudu a Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Da farko Arsenal ta nuna rashin kuzari abin da ya ba West Ham kwarin guiwa

Arsenal ta koma matsayin ta hudu a tebur bayan da ta doke West Ham United da ci 3-1, ta kawar da Everton a neman gurbin gasar Zakarun Turai.

Matt Jarvis ne ya saka bakin a gaba bayan da ya ci Arsenal da ka ana sauran mintina hudu a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma murnar 'yan West Ham din ba ta yi tsawo ba, domin mintina biyu tsakani ne sai Podolski ya rama wa Arsenal.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin ne kuma, a minti na 55 sai Olivier Giroud ya ci wa Arsenal kwallo ta biyu.

A minti na 78 ne sai Podolski ya sake jefa kwallonsa ta biyu kuma ta uku ta Arsenal, wadda ta jaddada komawar Arsenal matsayin ta hudu da maki 67 Everton kuma ta dawo ta biyar da maki 66.

Sai dai kuma Arsenal din ta yi wasanni 34 ne yayin da Everton za ta yi na ta na 34 din da Crystal Palace ranar Laraba.