'Yan wasan Swansea sun dambace

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Kungiyar Swansea na tangal-tangal a kakar wasa ta bana

Kungiyar Swansea City ta tabbatar da cewar wasu 'yan wasanta sun samu rashin jituwa a lokacin horo a sansaninsu da ke Wales.

Sai dai a cewar kungiyar duk da wannan hatsaniyar, tawagarta ta lashi takobin maida hankali wajen wasa don ci gaba da taka leda a gasar Premier ta Ingila.

Lamarin ya faru kafin wasan da Chelsea ta doke Swansea daci daya me banhaushi.

Kakakin Swansea ya ce "Tabbas akwai 'yan wasu matsaloli tsakanin wasu 'yan wasa amma an warware komai".

Swansea ta samu nasara a wasanni biyu cikin 13 ne tun bayan da Garry Monk ya maye gurbin Micheal Laudrup.

Karin bayani