Toure zai yi jinyar sati biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan na Ivory Coast ya ci kwallaye 22 a kakar bana

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya Toure zai yi jinyar mako biyu ta raunin da ya ji a wasan da Liverpool ta buge su ranar Lahadi.

Kociyan kungiyar Manuel Pellegrini ya ce, kila raunin bai kai tsananin da muka yi tsammani ba da farko amma dai yana bukatar akalla kwanaki goma zuwa sati biyu ya warke.''

Dan wasan na Ivory Coast da ya ci kwallaye 22 a bana, ba zai samu damar wasansu da Sunderland ranar Laraba ba da na West Brom da kuma na Crystal Palace, amma kyaftin din su Vincent Kompany da Aguero za su yi na Sunderland.

Manchester City tana matsayi na uku da bambancin maki bakwai tsakaninta da Liverpool ta daya, amma kuma da bashin wasanninta biyu.