Hart bai kai gwanin duniya ba- Shilton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption ''A yanzu dai yana kurakurai da dama musamman a wasannin Man City masu muhimmanci''

Tsohon mai tsaron gidan Ingila Peter Shilton ya ce golan kasar na yanzu Joe Hart ba ya daya daga cikin gwanayen duniya.

Sai dai kuma Shilton mai shekaru 64 wanda sau 125 ya yi wa Ingila wasa da har yanzu ba wanda ya zarta shi, yana ganin Hart mai shekaru 26 zai iya kaiwa wannan matsayi a duniya.

Tsohon golan ya ce, ''ba na jin a yanzu ya kai kokoluwa saboda har yanzu matashi ne, kuma kamar yadda muka gani a bana, yana yin kurakurai.''

''Amma duk da haka yana da kokari kuma Ina yabawa da kwazonsa.''