Man City ta sha wuya a hannun Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland ce ta karshe a tebur da maki 26

Manchester City ta barar da damarta ta rage yawan bambancin makin da ke tsakaninta da Chelsea da kuma Liverpool bayan da ta yi canjaras 2-2 da Sunderland.

Dan wasan Manchester City Fernandinho ne ya fara jefa kwallo a ragar Sunderland minti biyu da fara wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 73 Wickam ya rama wa Sunderland, bayan minti goma tsakani kuma sai ya kara kwallo ta biyu.

Ana saura minti biyu kuma lokaci ya cika sai Samir Nasri ya rama wa Man City kwallonta ta biyu.

Yanzu maki shida ne tsakanin City ta uku mai maki 71 da bashin wasa daya da Liverpool ta daya, kuma tana bayan Chelsea ta biyu da bambancin maki hudu.