Real Madrid ta dauki Copa del Rey

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne karo na 19 da Real Madrid ta dauki kofin

Real Madrid ta dauki Copa del Rey bayan da ta buge babbar abokiyar hamayyarta a Spaniya Barcelona da ci 2-1.

Angel Di Maria ne ya fara daga ragar Barcelona a minti na 11 da fara wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 68 sai Barcelona ta rama inda Barta ya daga ragar Real Madrid.

Sai dai kuma ana saura minti biyar lokacin wasan ya cika sai Gareth Bale ya jefa kwallo ta biyu ragar Barcelona.

Karin bayani