Hernandez zai bar Man U

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hernandez na ganin baya cikin tsarin Moyes wanda ya fifita Rooney da Van Persie da Welbeck a kansa

Manchester United ta gaya wa dan wasanta na gaba Javier Hernadez cewa a shirye take ta sayar da shi a wannan bazarar.

Kungiyar ta sheda wa dan wasan mai shekaru 25 hakan ne bayan da ya yi korafin rashin saka shi a wasanni a kai a kai.

Hernandez dan Mexico wanda ya buga wasanni 31 tare da cin kwallaye tara a bana kawai ana ganin zai koma Atletico Madrid domin maye gurbin Diego Costa wanda shi kuma ake sa ran zai koma Chelsea.

Tsohon dan wasan Guadalajara wanda Man United ta sayo shi a kan euro miliyan tara da dubu 700 a 2010 ya damu kan rashin samun damar kwarewa da kuzari yayin da gasar Kofin Duniya ke matsowa.

Yayin da kyaftin din kungiyar ta Manchester Nemanja Vidic ke shirin komawa Inter Milan, Rio Ferdinand da Patrice Evra da Shinji Kagawa da Nani da Anderson da Alex Butner su ma na daga 'yan wasan da ke shirin barin klub din.

Karin bayani