Howard ya sabunta kwangilarsa a Everton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Martinez ya jinjinawa Howard

Golan Everton, Tim Howard ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu don ci gaba da kasancewa a kungiyar har zuwa shekara ta 2018.

Dan wasan mai shekaru 35, ya hade da Everton daga Manchester United a shekara ta 2006.

Kocin Kungiyar Roberto Martinez ya ce "Labarin na da dadi. Kuma zai taimaka mana".

Howard ya kama wasanni 342 a Everton kuma ana saran zai kasance tare da tawagar 'yan kwallon Amurka a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Karin bayani