Neymar zai jinyar makonni hudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana saran Neymar zai haskaka a Brazil

Dan kwallon Barcelona Neymar zai yi jinyar akalla makonni hudu saboda rauni a kafarsa.

Dan wasan Brazil din mai shekaru 22 ya ji rauni ne a wasan da suka sha kashi a wajen Real Madrid a ranar Laraba.

Raunin Neymar zai kasance cikas ga Barcelona, bayan da aka fitar da Barcelona a gasar Zakarun Turai da kuma shan kashi a gasar Copa Del Rey.

Idan har ya murmure zai iya buga wasansu na karshe a kakar wasa ta bana, inda Barca za ta dauki bakuncin Atletico Madrid.

Neymar ya koma Barca ne daga kungiyar Santos ta Brazil a kan fan £48.6 a kakar wasa ta bana.

Ana saran zai kasance cikin tawagar Brazil a gasar cin kofin duniya da za a soma a watan Yuni.

Karin bayani