Dan wasan West Ham Tombides ya rasu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Margayi Dylan Tombides

Kungiyar West Ham ta tabbatar da mutuwar dan wasanta Dylan Tombides mai shekaru 20.

Kungiyar ta sanarda cewar Tombides wanda yake tare da ita tun yana dan shekaru 15, ya rasu ne sakamakon cutar cancer ta mafitsara

Tun a shekara ta 2011 ne, dan kwallon wanda haifaffen Australia ne ke fama da cutar cancer har zuwa ajalinsa.

Za a yi shuru na minti daya don juyayinsa a wasan da West Ham za ta dauki bakuncin Crystal Palace a ranar Asabar.

Karin bayani