Liverpool na gabda lashe gasar Premier

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Brendan Rodger ya jinjinawa Sterling

Liverpool na kan hanyar lashe gasar Premier ta Ingila a bana bayan da ta doke Norwich da ci uku da biyu a wasan da suka buga a ranar Lahadi.

Liverpool a yanzu ta baiwa Chelsea tazarar maki biyar a saman tebur, saboda Chelsea din ta sha kashi a hannun Sunderland.

Raheem Sterling ne ya ciwa Liverpool kwallaye biyu sai kuma Luis Suarez yaci kwallo daya a yayinda Gary Hooper da Robert Snodgrass suka ci wa Norwich.

Sakamakon sauran wasannin:

*Hull 0 - 3 Arsenal *Everton 2 - 0 Man Utd *Tottenham 3 - 1 Fulham *Aston Villa 0 - 0 Southampton *Cardiff 1 - 1 Stoke *Newcastle 1 - 2 Swansea *West Ham 0 - 1 Crystal Palace *Chelsea 1 - 2 Sunderland

Karin bayani