Liverpool za ta yi babban kamu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool na shirin nemo 'yan wasa

Kulob din Liverpool zai hari manyan 'yan wasa a kakar wasanni in ji Ian Ayre

Kulob din Liverpool zai baiwa manaja Brendan Rodgers damar nemo 'yan wasa a yayinda kulob din ke shirin gasar Champions League.

An ambato manajan daraktan kulob din Ian Ayre yana cewa za'a kashe ko nawa za'a kashe idan muka yanke shawarar kowa manaja yake son ya kawo.

Ian Ayre ya kuma ce idan ba a fafatawa da kai a matakin koluluwa, abune mai wahala nemo 'yan wasa.