'Man U ta nuna rashin kwarewa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption David Moyes ya godewa Sir Alex Ferguson

An zargi Kulab din Manchester United da nuna rashin kwarewa bayan korar David Moyes.

BBC ta fahimci cewa Moyes ya fusata game da yadda kulab din ya kore shi.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba Moyes ya ce yayi alfaharin shugabantar Kulab din, kuma ya godewa Sir Alex Ferguson saboda damar da ya bashi na zama shugaba.

Amma Kungiyar masu horar da wasan Premier League tace kulab din Manchaster United ya nuna rashin kwarewa a matakin da ya dauka.