Schole zai yi aiki tare da Giggs

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsaffin 'yan kwallon United

Paul Scholes zai hade da sauran masu horadda 'yan wasan Manchester United har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Scholes ya ki yarda ya yi aiki a karkashin David Moyes inda yace yanason ya zauna tare da iyalansa ya huta.

Amma a yanzu zai yi aiki tare da Ryan Giggs wanda shi ne kocin riko na Manchester United.

Giggs ya taka leda tare da Nicky Butt da Phil Neville da kuma Scholes a Old Trafford.

United a shafinta na Twitter ta ce "Muna murna Paul Scholes ya dawo sansanin horonmu".

A ranar Talata United ta kori David Moyes saboda kasa taka rawar gani.

Karin bayani