Terry da Cech za su yi jinya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Peter Cech

'Yan wasan Chelsea John Terry da Petr Cech ba za su kara buga gasar Premier a kakar wasa ta bana ba saboda rauni.

Dukkansu biyun sun ji raunin ne a wasansu da Atletico Madrid a gasar zakarun Turai a ranar Talata.

Terry ya ji rauni a kafarsa a yayinda shi kuma Cech ya samu targade a kafadarsa a wasan da suka tashi babu ci da Atletico Madrid.

Kocin Jose Mourinho ya ce Terry zai kara bugawa har sai idan Chelsea ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai.

Chelsea na kokarin lashe gasar Premier da kuma ta Zakarun Turai.

Karin bayani