An dakatar da Ramires na Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ramires ba zai taka wasanni hudu ba yanzu

Dan wasan tsakiyar Chelsea Ramires ba zai samu damar buga sauran wasannin Premier League ba, bayan daya amince da cajin da ake masa na rashin da'ar da ya nuna bayan da Sunderland ta doke su da ci 2-1 a ranar asabar din da ta gabata

Hakan na nufin an dakatar da dan wasan tsakiyar dan kasar Brazil daga buga wasanni hudu.

Manaja Jose Mourinho da kuma mataimakin sa Rui Faria suma na fuskantar caji daga hukumar FA daga wasan da kulab din ya taka da Sunderland.